30 Oktoba 2021 - 16:41
Sudan: Za A Nada Sabon Fira Minista Da Mambobin Majalisar Mulkin Kasa

Babban kwamandan rundunar sojin kasar Sudan Abdel Fattah Al-Burhan, ya bayyana cewa nan da mako guda za a bayyana sunayen sabon fira minista da kuma sabbin mambobin majalisar mulkin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A cikin wata zantawarsa da "Sputnik", wanda aka watsa a yau, Juma'a, Al-Burhan ya ce: "Ina fatan za a zabi Firayi Minista da mambobin Majalisar Mulki a cikin mako guda.

Dangane da zaben sabon firaminista, Al-Burhan ya ce, "Za mu zabi firaministan da zai kasance cikin masu fasaha," ya kara da cewa, "An zabi tsohon firaministan ne bisa yarjejeniya tsakanin bangarorin siyasa da na soja, yanzu kuma za a zabi firaminista ne bisa yarjejeniya tsakanin bangarori na soji.

Aaboda a cewarsa suna da wani nauyi na hakkin kasa wanda suke jagoranta da kuma taimaka wa a lokacin rikon kwarya har sai an gudanar da zabe.

A ranar Litinin din da ta gabata ne Al-Burhan ya sanar da kafa dokar ta-baci a kasar tare da rusa majalisar mulkin kasar da kuma gwamnatin rikon kwarya, yana mai zargin bangaren farar hula na hukumar da hada baki da wasu bangarori domin yi ma sojoji zagon kasa.

Haka nan kuma a ranar Litinin din ce dai rundunar sojin kasar ta cafke firaministan kasar Abdullah Hamdok, kafin daga bisani a sake shi, yayin da aka kama wasu 'yan siyasa da wasu jami'ai, amma kawo yanzu ba a sake su ba.

Matakan da Al-Burhan ya sanar sun janyo kakkausar suka daga kasashen duniya, tare da yin kira da a saki 'yan siyasa da jami'ai da ake tsare da su, da kuma komawa kan turbar dimokuradiyya.

342/